Rijiyar ta kusugu dai ta na da dimbin tarihi wanda ake alakantawa da Bayajidda, wani jarumin maza da ake ta’allakawa da tarihin asalin Hausawa, wanda kuma ake cewa ya kashe wata macijiya da ke hana mutane diban ruwar rijiyar ta Kusugu in ba ranar Juma’a ba.