Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Takaddamar Gwamnan Neja Da Mataimakinsa Na Kara Muni


Gwamna Mu'azu da Atiku a lokutan baya.
Gwamna Mu'azu da Atiku a lokutan baya.

Takaddamar Gwamna Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Naija da Mataimakinsa Alhaji Musa Ebito, wanda ya bar PDP zuwa APC, ta kara tsanani har ta kai ga rashin kasancewar Ebito a taron Majalisar Jihar.

Mataimakin Gwamnan na mai da martani ne game da sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar cewa shi Mataimakin Gwamnan jihar da kansa ne ya bukaci a masa uzuri daga halartar taron Majalisar Jihar. Yace, “A hakikanin gaskiya, shi Gwamnan Naija ne y ace ba zai yiwu a zauna a yayin da su ke gudanar abubuwa na Majalisar jiha ba, saboda ni ba dan jam’iyyar PDP ba ne. Alal hakika, ya iya nuna cewa ma, hasali, an kawo mashi “recording” na inda na ke cewa shi barawo ne da sauransu; kuma na tashi na ce ba haka ba ne.”

Da wakilnmu na Naija, wanda ya aiko da rahoton Mustafa Nasiru Batsari, ya tambaye shi matsayin da ya dauki kansa, sai y ace har yanzu shi ne Mataimakin Gwamnan jihar Naija kuma har yanzu shi mamba ne a Majalisar Jihar.

Da Mustafa ya tambayi wani lauya mai suna Abdulmalik Sarkin Daji matsayin wannan takaddamar a kundun tsarin mulkin Nijeriya, sai ya ce lallai Gwamna na da dinbin iko, to amma bai da ikon hana Mataimakinsa zama a Majalkisar Jihar saboda shi ma Mataimakin mamba ne. Y ace don kawai Mataimakinsa ya canza sheka, Gwamna bai da hurumin hana shi zama a Majalisar jiha.

Takaddamar Gwamnan Neja da Mataimakinsa na Kara Muni - 3'18"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG