Mai-alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na 3, yayi kira ga ‘yan Najeriya su dage wajen tabbatar da ganin kasar ta ci gaba da zama lafiya, saboda duk wani abu sabanin haka ba Alheri bane ga kasa da al’umarta.
Sarkin Musulmin yayi wannan kiran ne a ranar Laraba, lokacinda ya karbi bakuncin shugabannin hukumomin tsaro da na kabilu dake zaune a Sokoto.
Alhaji Abubakar Sa’ad yace ko kallo mutum yake yi a talabijin, abubuwa da suke faruwa a kasashen da ake rikici na kusa kamar Libya, da Sudan da kudu, da kuma a Syria, da Iraqi, da Afghanistan, ba yanayi bane mai kyau da mutum zai so ya gani a kasarsa.
Tunda farko kwamishinan ‘Yansanda na jahar Sokoto Mohammed Abdulkadir ya gana da shugabannin kabilu da suke da zama a sokoto. Ya basu tabbacin cewa hukumarsa shirye take ta kare lafiya da dukiyoyinsu.
Abdulkadir ya gaya musu cewa Najeriya ta dukkan ‘yan kasar ce, kuma kowa yana da ‘yancin ya zauna a duk yankin kasar da ya ga dama.
Facebook Forum