Wani kamfanin dillancin labaran kasar Sudan yace dakarun gwamnati sun sake kwace ikon garin Girayda dake hannun ‘yan tawaye a yankin Darfur mai fama da tashin hankali a yammacin kasar.
Cibiyar sadarwa dake magana a wadansu lokuta da yawun gwamnati, ta ambaci wadansu jami’an gwamnati na cewa, C mai tazarar kilomita dari a kudu da Nyla, babban birnin Jihar Darfur ta Kudu.
Jami’ai sun ce har yanzu ana ci gaba da gumurzu, gwamnati kuma ta tura karin dakaru a yankin.
‘Yan tawayen sun musanta cewa, an kore su daga yankin, sai dai dakarun kiyaye zaman lafiya na hadin guiwa tsakanin Kungiyar hadin kan Afrika da Majalisar Dinkin Duniya a Darfur (UNAMID) , sun ce sun lura da abinda ya biyo bayan fadan. Kakakin UNAMID yace tawagar kiyaye zaman lafiyan taga gawarwaki da dama, yayinda kuma aka yi barnar gaske a garin.