Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Soke Kauracewa Isra’ila


White House
White House

Majalisar Kolin Sudan da Majalisar Ministocin kasar a kwanan nan sun kada kuri’ar soke kauracewar Isra’ila da suka kwashe sama da shekaru shida su na yi. Dokar ta hana kafa dangantakar diflomasiyya da Isra'ila kuma ta hana duk wata huldar kasuwanci da kasar ta Yahudu. Hukuncin waɗanda suka yi cinikayya da Isra’ilawa, ya haɗa da daurin shekaru 10 a kurkuku da tara mai tsanani.

"Amurka na maraba da sanarwar," in ji mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Ned Price. "Wannan wani muhimmin mataki ne da zai samar da sabbin dama ga mutanen Sudan, Isra'ila, da kuma fadin yankin."

Sanarwar ta kara sa ake kara kusantar daidaita dangantaka tsakaninSudan da Isra’ila bayan sanya hannu kan yarjejeniyar Abraham da Amurka a watan Janairu.

A watan Agustan 2019, mutanen Sudan suka hambarar da Omar al-Bashir wanda yadade yana mulkin kama-karya. Kasar yanzu tana karkashin gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula wacce ke neman kyakkyawar alaka da kasashen yamma da ci gaban tattalin arziki. Tattalin arzikin Sudan ya yi fama da rashin tsari na tsawan shekaru karkashin al-Bashir, wanda ya yi mulki kasar tun bayan juyin mulkin soja na 1989 da masu kishin Islama suka yi. Haka kuma Sudan ta yi kauri suna a matsayin mai tallafawa ta'addanci a cikin shekarun 1990s domin karbar bakuncin shugaban kungiyar al-Qaeda Osama bin Laden da sauran 'yan ta'adda da ake nema.

Matakan da sabbin shugabanni suka dauka a Sudan don kawo karshen goyon bayan kasar ga ayyukan ta'addanci na kasa da kasa ya ba Amurka damar soke ayyukanta na Sudan a matsayin kasa mai daukar nauyin ta'addanci a watan Disambar 2020.

An sanya hanu kan karin yarjejeniyar daidaituwa a shekarar da ta gabata tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da ma Bahrain. Haka kuma Morocco ma ta kulla huldar jakadanci da Isra’ila.

"Muna farin cikin maraba da wannan sabon zamanin a alakar Sudan da Isra'ila," in ji mai magana da yawun Price, "kuma muna sa ran ganin karshen abun da kauracewar zai haifar."

XS
SM
MD
LG