Jami’ai a Khartoum babban birnin Sudan sun ce yawan cin zarafin mata da yara a cikin gida ya karu a lokacin da aka takaita zirga-zirga sakamakon annobar cutar COVID-19.
Sulaim Al Khalifa, shugabar Ofishin sa ido akan harkokin jinsi a ma’aikatar kula da jin dadin rayuwar al’umma, ta ce ofishinta ya shigar da bayanan rahoton cin zarafin da ya shafi jinsi a cikin gida guda 42, ciki har da fyade, da dukan mata da yara mata a Khartoum da kuma wasu garuruwan a fadin Sudan a cikin watan da ya gabata.
“Bayanan cin zarafin na zuwa daga ko ina a fadin Sudan, amma galibi sun fi zuwa daga birnin Khartoum, kuma yawanci cin zarafin da ya faru a cikin gida ne."
"An samu inda aka daure wasu aka kuma kulle su a wani daki, mun kuma san akwai wasu abubuwan da suka faru da ba su zo kunnuwanmu ba," a cewar Al Khalifa a shirin South Sudan in Focus na Muryar Amurka.
A karkashin mulkin tsohon shugaba Omar Al Bashir da ya yi tsawon shekara 30, babu wasu dokoki da za su kare mata da yara mata, lamarin da ya jefa su cikin yanayin da za a iya cin zarafinsu a tsakanin iyalansu.
Facebook Forum