Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sokoto: An Kai Hari Sabon Gari a Ranar Sallah


Gawarwakin Wasu Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Kashe a Sokoto Cikin Kwannakin Baya
Gawarwakin Wasu Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Kashe a Sokoto Cikin Kwannakin Baya

A daidai lokacin da al'ummar Musulmi a fadin duniya ke shagulgulan sallah karama, al'ummomi a yankin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto a arewacin Najeriya suka fuskanci wani tashin hankali.

A cewar wasu wadanda suka sheda harin mahara sun fito ranar sallah dauke da bindigogi, suka rinka harbin mutane.

Saboda tsananin harin, sai da aka dukkufa wajen tsintar gawarwaki na mutanen da 'yan bindigan suka kashe.

Wani wanda ya sheda aukuwar lamarin, ya sheda wa Muryar Amurka cewa, “mutanen sun fito ne daga cikin wani daji wanda ke tsakanin Sabon Birni da garin Bature, inda suka hana kowa wucewa.

“Da muka lissafa gawarwakin mutanen da aka kashe, muna kan 14 a yanzu.”

Yayin da yake tsokaci kan harin, Kwamishinan tsaro a jihar ta Sokoto, Kanar Garba Moyi mai ritaya ya ce “maharan suna karanta yadda ake tsara wuraren da ake aika sojoji.”

“Ba zai yi wu a ajiye sojoji a kowanne kauye ba, suna lura da yadda sojojin ke tafiya daga kauye-kauye ne kafin su yanke shawarar inda za su kai hari.”

A cikin ‘yan kwannakin nan yadda ake kai hare-hare a yankin na kara kaimi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG