Kakakin rundunar tsaron sojin Najeriya Manjo Janaral Cris Olokolade yace sunyi amanna sun sami gagarumar nasara akan hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa kuma suna samun sakamako mai kyau ta wajan kwato wurare da dama da hannun ‘yan kungiyar boko haram , kuma hakan zai bada dama ga jama’ar yankin da suka yi gudun hijira dan tsira da ransu kuma su koma gidajen su.
Shugaba Jonathan ma ya kai ziyarar bazata a garin Baga da Mubi a makon da ya gabata kuma wajan na hannun mayakan kungiyar boko haram ne a da. Kuma tabbas ‘yan gudun hijirar na farin ciki da nasarorin da ake samu, saidai suna da sauran fargaban koma wa gida musamman saboda ganin yadda ake korar ‘yan ta’addar amma su sake komawa.
Da alamu dai nasarar da dakarun Najeriya ke samu na da nasaba ne da sojojin makwabta da suka raraki ‘yan bindigar daga iyakar kasar. A wata hira da wakilin muryar Amurka Nasir Adamu El’hikaya yayi da Janar Mansur Dan Ali mai ritaya , yace “shigowar sojojin ba bisa ka’ida bane”.