WASHINGTON, DC —
Wani jami'in sojan Najeriya yace dakarunsu sun bindige suka kashe wani mutumin da ake kyautata zaton cewa mai magana da yawun kungiyar nan ta Jama'atu Ahlul Sunnati Lilddaawati Wal Jihad ce, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, sannan suka kama wasu manyan jami'an kungiyar guda biyu.
Kakakin rundunar tsaro ta hadin guiwa a Kano, Leftana Iweha Ikedichi, ya fadawa 'yan jarida cewa a yau litinin suka kai farmaki kan wani gida dake Hotoro, inda aka yi arangama da mutanen.
Kakakin ya ki ya bayyana sunan wanda aka kashe, ko wadanda aka kama, amma ya tabbatarwa da 'yan sanda cewa shugabanni ne a kungiyar ta Boko Haram.
Har yanzu ba a ji ta bakin kungiyar a kan wannan lamari na yau litinin ba.