Rahotanni daga Najeriya na fadin cewa sojoji sun bude wuta a kan masu gangamin Ranar Qudus a Zaria, Jihar Kaduna, suka kashe mutane 11, cikinsu har da dan jagoran Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.
Ba a san dalilin da ya sa sojojin suka bude wuta kan wadannan masu zanga-zangar da suka saba yin irinta kowace shekara a ranar 25 ga watan Yuli ba.
Rahotanni daga Zaria na cewa an harbe aka kashe Mahmud Zakzaky tare da wasu mutanen su 10, cikinsu har da wata mace mai goyo a bayanta.
Musulmi 'yan mazhabin Shi'a su na gudanar da gangamin Ranar Qudus a kowace shekara a fadin duniya, domin nuna goyon bayansu tare da jajantawa Falasdinawa dake karkashin mamayar kasar Isra'ila.
A bayan Zaria ma, an gudanar da irin wannan gangami a manyan birane da dama na Najeriya ba tare da samun tashin hankali ba.
Har ya zuwa yanzu ba a ji ta bakin hukumomin soja ko jami'an gwamnatin Najeriya a kan wannan lamarin ba.