An fara bukukuwan taron shuwagabanin kasashen Afirka, da shugaban Amurka Barack Obama, a birnin Washington.
A wajen wani taron da akayi dasu kan shirin bunkasawa da samar da dama a Afirka, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, yayi kira ga ministocin Afirka da su rungumi akidar walawlar kasuwanci da hadin kai tsakanin Afirka da Amurka.
An shirya sakataren zai gana da shuwagabanin kasashen Afirka takwas a yau litinin.
A gobe talata,shugaba Obama zai yi jawabi ga wani taron kasuwanci a tsakanin Amurka da Afirka, zai kuma shiga cikin tarurukan da za’a yi ran laraba akan bunkasar tattalin arziki, tsaro da kuma gudanar da mulki na kwarai.
A wani hira da babban edita shashen hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha, yace duk da yake ba duka shuwagabanin da ake sa ran zasu suka riga suka shigo ba akwai wadanda ake sa ran sai yau zasu shigo.
Yace koda yake shuwagabanin Sierra Leone, Guinea da Liberia batun Ebola ya hana su zuwa.Ya kara dacewa taron na kwanaki uku ne amma inda Allah ya kai mu ranar laraba wace itace ranar karshe ranar za’a ayi maganar daya daga cikin manyan matsalolin da kasashen mu na Afirka suke fuskanta wato maganar tsaro da kuma samae da zaman lafiya.