Shugabannin Afirka ta Yamma sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kara irin ikon da ta ba rundunar kiyaye zaman lafiyarta a kasar Ivory Coast, ta kuma kafa takunkumi a kan shugaba Laurent Gbagbo. A cikin sanarwar da ta bayar jiya alhamis, Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta kuma yi kira ga ofishin kula da ayyukan MDD a kasar Ivory Coast da ya samar da sukunin mayarda mulki ga mutumin da duniya ta yarda da cewa shi ya ci zabe, Alassane Ouattara, daga hannun Mr. Gbagbo. ECOWAS ta bayar da wannan sanarwa a bayan taron kolin shugabanninta a Abuja, babban birnin Najeriya. Wani jami’in kula da hakkin bil Adama na MDD a Abidjan, Guillaume Ngefa, ya zargi sojojin Mr. Gbagbo da laifin yin luguden wuta da gangan a kan yankunan da ake gani na magoya bayan Mr. Ouattara ne. Ngefa yace a cikin mako gudan da ya shige, an kashe mutane akalla 50 a irin wannan lugudenw uta, ciki har da yara kanana su biyar, abinda ya sa adadin wadanda aka kashe a tashin hankalin da ya biyo bayan zabe ya kai 462. Gwamnatin Gbagbo ta musanta yin amfani da manyan makamai a kan fararen hula, ta kuma zargi MDD da laifin nuna goyon baya ga Mr. Ouattara.
Shugabanin kasashen Afrika ta yamma sunyi kira ga Majalisar Dinkin Duniya data kara irin ikon data baiwa rundunar kiyaye zaman lafiya a Ivory Coast
Shugabannin Afirka ta Yamma sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kara irin ikon da ta ba rundunar kiyaye zaman lafiyarta a kasar Ivory Coast, ta kuma kafa takunkumi a kan shugaba Laurent Gbagbo. A cikin sanarwar da ta bayar jiya alhamis, Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta kuma yi kira ga ofishin kula da ayyukan MDD a kasar Ivory Coast da ya samar da sukunin mayarda mulki ga mutumin da duniya ta yarda da cewa shi ya ci zabe, Alassane Ouattara, daga hannun Mr. Gbagbo.