Mutanen Tanzania na can suna ta nuna damuwa da yi wa juna tambayoyi gameda halin lafiyar shugaban kasar tasu, Jakaya Kikwete, wanda ya fadi, ya some a lokacinda yake kaddamarda bikin soma kyamfen dinsa na neman zabe a ranar Assabar da ta gudana. Rahottani sunce shugaba Kikwete ya yanke, ya fadi ne a lokacinda yake cikin yiwa dubban magoya bayansa jawabi a birnin Dar-es-Salam. Sai dai wasu sunyi sauri sun cafke shi kafin ya fadi kasa, kuma bayan ya fita, bai dade ba, ya dawo, yace ala-tilas sai da ya karya azuminsa. Wannan dai shine karo na ukku da shugaba Kikwete, dan shekaru 59 da haihuwa, yake taba faduwa, yana somewa a bainar jama’a. A shekarar 2005 an taba irin wannan, a lokacinda shugaban ya fadi a cikin wannan filin wasan da abin ya faru a wannan karon. Sannan kuma ya sake maimaita irin hakan a watan Oktoban da ya gabata. Shine yanzu al’ummar Tanzania ke neman shugaban ya gaya musu gaskiya idan yana fama da wata matsala ta rashin lafiya.
Al’ummar Tanzania sun fara shakku gameda isasshiyar lafiyar shugabansu, bayanda ya sake faduwa, ya some a gaban bainar jama’a.