Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan Da Na Sudan Ta Kudu Sun Tattauna


Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya na sauraren shugaban Sudan Ta Kudu Silva Kiir a wajen wani taron manema labaran hadin guiwa a filin jirgin saman Khartoum kafin Mr.Kiir ya tashi zuwa gida bayan ya kammala ziyarar aikin kwanaki biyu.
Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya na sauraren shugaban Sudan Ta Kudu Silva Kiir a wajen wani taron manema labaran hadin guiwa a filin jirgin saman Khartoum kafin Mr.Kiir ya tashi zuwa gida bayan ya kammala ziyarar aikin kwanaki biyu.

Shugaba Salva Kiir da Omar Hassan al-Bashir sun tattauna wasu matsalolin da ke ci gaba da kawo cikas

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya kammala ziyarar aikin kwana biyu a Khartoum inda shi da shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir su ka tattauna wasu matsalolin da ke ci gaba da haifar da tankiya tsakanin kasashen biyu.

Matsalolin da aka kasa warwarewa tun da Sudan ta Kudu ta samu ‘yancin kan ta a farkon watan yuli su ne makomar yankin Abyei mai arzikin man fetur wanda kasashen biyu ke takaddama a kai, da kuma batun raba kudin man wanda akan shi kasashen biyu su ka dogara.

A yayin wata ganawa da manema labarai a yau lahadi, shugabannin biyu sun fada cewa za a kafa kwamitoci a wani kokarin neman ganin bayan takaddamar wadda ta haifar da fargabar cewa kar kasashen biyu su sake fadawa cikin yakin basasa. Mr.Kiir ya ce gwamnatin shi a shirye ta ke ta tattauna hanyoyin warware illahirin manyan matsalolin da su ke fuskanta. Shugaba Bashir ya ce an bada wa’adi. Amma bai yi wani karin bayani ba.

Akasarin man fetur din ya na kasar Sudan ta Kudu, amma ta na bukatar cibiyoyin kasar Sudan na cikin tekun Maliya, wajen fitar da man na ta kasashen waje.

Ma’aikatan diflomasiya sun ce yardar da shugabannin biyu su ka yi, su ka gana da juna, wata alama ce kyakkyawa.

XS
SM
MD
LG