Asma'u Bawa ta yi hira da shi kai tsaye a talabijin, inda ya bayyana makasudin ziyarar tasa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a inganta aikin jarida baki daya da kuma zamantakewar mutane.
Daga Hijira TV tawagar ta Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto ta tafi gidan radio Marhaba 99.3 FM.
Nan ma Alhaji Aliyu yayi hira da shugaban tashar, Alhaji Baba Shariff akan yadda aikin radio ke tafiya da kuma yadda VOA ke taimaka wa tashar da shirye shiryenta da ake yadawa a tashar tare kuma da zummar inganta huldar da ke tsakanin tashoshin VOA da Marhaba.
Abin da ya kara wa ganawar armashi shi ne hira da Babaa Sharif ya yi da Alhaji Mustapha Sokoto a studio marhaba, inda hira ta kai har ga manufofi da ajenda na voa Hausa.
A karshe an bai wa masu saurare dama, inda suka nuna farin cikinsu da wannan ziyara na shugaban VOA Hausa.
Tuni dai ya shiga birnin Kumasi jihar Ashanti ya wuce zuwa jihar Arewaci inda ya dawo birnin Accra ya sadu da sarakunan Hausawa, sai kuma Sheikh Dakta Usman Sharubutu, sannan yayi bankwana da al’ummar Ghana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: