Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Riko Dioncounda Traore Ya Bayyana Sabon Garambawul


Shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Dioncounda Traore.
Shugaban rikon kwarya na kasar Mali, Dioncounda Traore.

Shugaban riko na Mali yace duk wanda yake rike da babban mukami a gwamnatinsa ba zai yi takara a zaben da gwamnatin zata shirya ba

Shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore, ya bayyana shirye-shiryen yin garambawul ga gwamnatinsa, ya kuma nemi taimakon kasashen ketare wajen sake kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan kishin Islama.

A cikin jawabin da yayi ta telebijin ga al'ummar kasar a daren lahadi, Mr. Traore yace zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya mai mataimakan shugaban kaaa guda biyu har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe. Ya ce shugaban kasa, da firayim minista da sauran ministocin gwamnati ba za su shiga takarar wata kujera a zabubbukan da za a shirya ba.

Wannan jawabin shi ne na farko da yayi ga al'ummar kasar Mali tun ranar Jumma'a, lokacin da ya koma kasar daga jinyar da yayi a kasar Faransa. A watan Mayu ne 'yan zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati suka kutsa cikin fadar shugaban kasar, suka lakkada ma Mr. Traore duka a cikin ofishinsa.

A cikin jawabin nasa na lahadi, shugaban yace kasar Mali tana wani muhimmin gacci a rayuwarta.

A bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 22 ga watan Maris, 'yan awaren kabilar Abzinawa da 'yan kishin Islama sun kwace yankin arewacin kasar. A cikin 'yan kwanakin nan, 'yan kishin addinin masu alaka da kungiyar al-Qa'ida, sun kara jaddada matsayinsu a sassan arewaci.

A kudancin kasar kuma, akwai damuwa a game da hadin kai da kuma kwanciyar hankali a cikin ita kanta gwamnatin rikon da kuma ikirarin cewa har yanzu sojojin da suka yi juyin mulki su na yin katsalanda a cikin harkokin gwamnati.

Ana sa ran cewa Mr. Traore zai nemi Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura wata tawagar sojojin kasashen waje domin ta taimaka wajen maido da oda a kasar Mali. Kungiyar ECOWAS ta ware sojoji kimanin dubu 3 da 300 domin girka su a kasar ta Mali.

XS
SM
MD
LG