Duk inda aka yi kasar da babu doka da oda to zata lalace. Duk da matsalar da kasar ta shiga mahukuntar kasar so suke su kara dulmuyar da kasar cikin rudani.
Shugabannin tsaro da suka bari ana anfani dasu abun kunya suka zama ga kasar da al'ummarta. Sun kada girman makamansu sun kuma wulakantar da kansu. An aika mutum ya aikata abun da ba daidai ba ya maida kansa tamkar damba.
Gwamna Wamakko yace zasu dauki matakan kalubalantar abun da ya faru a majalisar dokoki. Maimakon gwamnati ta zama kan gaba wurin kawo zaman lafiya sai gashi ita ce ke haddasa rikici domin cimma muradun mutum guda.
Dokar ta baci bata hana komi ba. Sabili da haka babu anfanin sake sabuntata domin bata yi tasiri a jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba.
Ga karin bayani.