Karo na uku ke nan da shugaba Muhammad Buhari zai gabatar da kasafin kudi a gaban hadakar majalisun tarayya tun daga lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015.
Kasafin na Naira tiriliyon takwas da digo shida ya zama kasafi ma fi tsoka a tarihin Najeriya da aka yiwa lakabin kasafin farfado da tattalin arzikin kasar.
Sanata Abdullahi Gumel yace wannan kasafin kudin yana yiwa ‘yan Najeriya alkawarin cewa wahala ta kare, lokacin jin dadi ya karato saboda wai kasafin kudin na kunshe da abubuwa na more rayuwa.
Kasafin ya nuna kanana ayyuka zasu lakume Naira tiriliyon uku da digo hudu kana manyan ayyuka na da tiriliyon biyu da digo hudu. An bayyana adadin kudaden da za’a kashe akan ayyuka daban daban.
Amma a kan batun gina ko gyara hanyoyi shugaba Muhammad Buhari yace tuni har an gina hanyoyi fiye da kilomita dari bakwai .
Sanata Ibrahim Kabiru Gaya shugaban kwamitin dake kula da hanyoyi na majalisar dattawayace karin kudin da aka yiwa gina hanyoyi ci gaba ne matuka. Ya yaba da kasafin kudin.
Amma daya daga cikin dan jam’iyyar APC, matashi Kalib Ismail wanda aka gabatar da kasafin a gabansa ya ce ana kitso da kwarkwata saboda a cewarsa kasafin kudin wannan shekarar ta 2017 babu wani abun a zo a gani da gwamnatin ta yiwa ‘yan Najeriya. Ya ce haka ma ya faru da kasafin kudin shekarar 2016.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum