Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majami’ar Methodist Ya Ce An Biya Makudan Kudin Fansa Kafin a Sake Shi


Samuel Kanu Uche
Samuel Kanu Uche

Biyo bayan sakin shugaban majami’an Methodist a Najeriya da aka sace, shugaban ya bayyana cewa sai da cocin ta biya kudin fansa na kusan kwatan miliyan na dala kafin a sake shi.

Shugaban majami’ar, Samuel Kanu-Uche, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Legas a ranar Talata, jim kadan bayan an sako shi.

Kanu-Uche ya ce cocin ta biya kimanin dala 240,000 a matsayin kudin fansa ga wadanda suka sace shi domin a samu ‘yancinsa da na fastoci biyu da ke tafiya tare da shi.

Wasu mutane 8 dauke da makamai suka yi musu kwanton bauna a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama a jihar Abia a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta harbe-harbe kan motar da suke ciki kafin su yi garkuwa da su. Direban limaman cocin da wani dan cocin daya sun tsira daga harin.

Kanu-Uche ya ce masu garkuwa da mutanen sun nuna masu gawarwakin wadanda aka yi garkuwa da su a baya wadanda suka kasa biyan kudin fansa sannan su ka yi masu barazanar hakan suma idan ba a biya ba.

Har yanzu hukumomin Najeriya ba su ce uffan ba game da sakin sa. Sai dai jami'ai sun sha nuna rashin amincewarsu da biyan kudin fansa ga wadanda aka yi garkuwa da su, inda suka ce kudaden na kara karfin wadanda suka sace.

Archbishop Chibuzo Opoko shine shugaban cocin Methodist a jihar Abia. Yace biyan kudin fansa ya zama dole.

“Da ba a yi haka ba da ba za su sake mu ba. Ba jami’an tsaro ne suka shiga tsakani ba,” inji shi. "Yaya wannan doka za ta yi tasiri yayin da jami'an tsaro ba sa yin iya kokarinsu? Mece ce doka ga masu yin garkuwa da mutane da neman kudin fansa?"

A kokarin da take yi na dakile sace-sace, a kwanakin baya ne majalisar dattawan Najeriya ta amince da dokar da za ta hukunta biyan kudin fansa da daurin shekaru 15 a gidan yari.

Kudirin dokar zai kuma hukunta masu garkuwa da mutane da hukuncin kisa idan wanda aka sace ya mutu a hanunsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil' adama da iyalan wadanda aka sace na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da matakin. Daga cikin su akwai Abdulfatai Jimoh, mai magana da yawun iyalan fasinjojin da aka sace daga wani jirgin kasa a jihar Kaduna a karshen watan Maris.

“Wannan kudiri ne da ba shi da tsari. Ana samun irin wannan kudirin ne a kasar da ta ke da doka kuma dokar ta ke aiki. Inda har aka yi garkuwa da wani, sai a ceto wannan mutumin cikin sa’o’i 48, ba tare da bacin lokaci ba. Idan ko babu irin wannan dokar, to ta yaya za a hana mutane biyan kudin fansa," in ji shi.

Har yanzu dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai bayyana ko zai sanya hannu kan kudurin dokar ba.

Idan ba a manta ba, wasu ‘yan bindiga ne suka yi awon gaba da shugaban a ranar Lahadi a lokacin da yake tafiya a jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Biyan kudin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran shugaban Najeriyar zai rattaba hannu kan kudirin dokar hukunta wadanda suka biya kudin fansa daurin shekaru 15 a gidan yari.

XS
SM
MD
LG