WASHINGTON, D.C. - Marigayi wanda yake dadaddan ‘dan siyasa ne sosai an zabe shi a majalisar dokokin jihar a shekarar 2003 domin wakiltar karamar hukumar Karasuwa ta jam’iyyar PDP, baya ga haka kuma lokacin zaben gwamna na 2015 a jihar, Gana ya rike matsayin mataimakin ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP amma ya koma jam’iyyar APC a shekarar 2019.
Wani abokinsa na kusa Ado Adamu Bomboy, ya bayyana marigayin a matsayin mai gaskiya, mai barkwanci, mai aiki da gaskiya, mai tawakali, kuma shugaba mai aiki wanda ba za a iya mantawa da shi nan kusa ba.