Shugaban kwamitin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa domin shirya sulhu da ‘ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnati Lidda’awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, Barrister Kabiru Tanimu Turaki, ya lashi takobin cewa duk wani abinda zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar Arewa da ma Najeriya baki daya, zasu yi shi.
Barrister Turaki, wanda shi ne ministan ayyuka na musamman na Najeriya, yace su na samun ci-gaba a ayyukan da suke yi na shirya sulhu, domin su na samun hadin kai da taimakon ‘yan Najeriya. Ya ce da gaske ne akwai wasu mutanen dake fakewa da sunan wannan kungiya su na aikata wasu laifuffuka, kamar fashi a bankuna, amma kuma duk da haka ba zasu kasa iya gudanar da aikinsu ba.
Yace ganin irin nasarorin da suke samu, lallai hakar kwamitinsu zai kai ga cimma ruwa. Sai dai ya ki bayyana irin wadannan nasarorin da suka samu, yana mai fadin cewa yin hakan zai iya kawo cikas ga ayyukan da suke yi.
Ya yaba ma ‘ya’yan kwamitin, yana mai fadin cewa mutane ne masu kishi da kudurin wanzar da zaman lafiya a Najeriya.
Barrister Kabiru Tanimu Turaki, yana magana ne cikin wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka. Ga bayaninsa.