Shugaban kungiyar hadin kan kasashen Afrika yana kan hanyarsa zuwa kasar Ivory Coast yau Talata a yunkurin shiga tsakani dangane da rudamin siyasar da kasar ke ciki. Ana kyautata zaton shugaban kasar Malawi Bingu wa Mutharika zai gana da shugaban kasar Ivory Coast mai ci yanzu Laurent Gbagbo da kuma Alassane Quattara wanda kasashen duniya suka hakikanta cewa shine ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Nuwamba. Za a yi wannan zaman ne bayan shiga tsakani karkashin jagorancin PM kasar Kenya Raila Odinga da bai cimma nasara ba. Kungiyar Tarayyar Afica tana matsawa Mr. Gbabgo lamba ya mika mulki, sai dai kawo yanzu ya yi watsi da wannan kiran. A wata dabam kuma, manzannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, zasu zo nan Amurka wannan makon domin tattaunawa da shugaban Barack Obama da kuma babban magatakardan MDD Ban Ki- Moon. Jiya Litinin ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya yace kungiyar ECOWAS tana neman izini daga kwamitin sulhu na MDD domin tayi amfani da karfi soji a Ivory Coast. Kungiyar ta yi barazanar daukar matakin soji idan ta kama wajen kawar da Mr. Gbagbo daga karagar mulki.
Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika zai je Ivory Coast domin tattaunawa da shugabannin kasar biyu dake adawa da juna
Shugaban kungiyar hadin kan kasashen Afrika yana kan hanyarsa zuwa kasar Ivory Coast yau Talata a yunkurin shiga tsakani dangane da rudamin siyasar da kasar ke ciki