Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Zimbabwe ya tsallake rijiya da baya


shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, wa wajen gangamin yakin neman zabe
shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, wa wajen gangamin yakin neman zabe

Shugaban kasar Zimbabwe ya tsallake rijiya da baya a wata fashewa da ta auku a wajen gangamin yakin neman zabe

Emmerson Mnangagwa ya fada jiya asabar cewa, "fashewar ta auku ne a dab da ni, sai dai lokacina baiyi ba."

Fashewar ta auku ne bayan ‘yan dakiku da Mnangagwa ya kammala jawabi a filin wasan dake Bulawayo da ya cika makil, inda ‘yan hamayya suka fi karfi.

Shugaban kasar ya bayyana cewa, an yi ta yunkurin hallaka shi, kuma yanzu abin ya zamar mashi jiki.

Tashar talabijin ta kasar tace mutane arba’in da biyu suka ji rauni a fashewar, da suka hada da mataimakin shugaban kasa.

Nan da nan babu wanda ya dauki alhakin harin.

Shugaban adawa Nelson Chamisa ya buga a shafinsa na twitter cewa, “tashin hankali bashi da wurin zama a siyasarmu.”

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG