Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Togo Ya Ziyarci Shugaba Buhari na Nigeria


Shugaban Togo Gnassingbe Eyadema da Shugaba Buhari na Najeriya
Shugaban Togo Gnassingbe Eyadema da Shugaba Buhari na Najeriya

Shugaban Togo Gnassingbe Eyadema wanda shine shugaban kungiyar ECOWAS ya gana da shugaban Najeriya Muhammad Buhari a kebe kafin ya zanta da ‘yan jarida

Bayan shugaban kasar Togo Gnassingbe Eyadema ya gana da shugaban Najeriya cikin sirri ya yiwa manema labarai karin bayani inda ya bayyana abun da ya kawoshi Najeriya.

Shugaban Togo Gnassingbe Eyadema da Shugaba Buhari
Shugaban Togo Gnassingbe Eyadema da Shugaba Buhari

Shugaban Togon ya ce ya zo Najeriya ne domin ya gana da shugaba Buhari ya kuma gode masa kan yadda ya taimaka a zaben sa a matsayin shugaban ECOWAS tare da nuna farin cikinsa bisa lafiyar da shugaba Buhari ya samu yanzu.

A cewar Shugaba Eyadema ya tattauna da shugaban Najeriya akan batutuwan da suka shafi kasashen yammacin Afirka. Kazalika sun duba batu matsalar tsaro a kasashen Liberia, da Guinea Bissau da kuma Togo.

Ta bakin tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Ambassador Suleiman Dahiru, babu abun da Najeriya ba zata iya yi ba game da bada taimako. Yana cewa duk abun da shugaban Togo yake son Najeriya tayi, zata yi domin ta fi karfin bukatarsa. Yace duk abubuwan dake faruwa a kasashen ECOWAS Najeriya zata iya shiga tayi abun da ya kamata. Ya bada misali da rigingimun Liberia da Saliyau inda Najeriya ta kashe miliyoyin daloli tare da hasarar sojojinta.

Shugaban Togon ya himmatu akan yadda ECOWAS ta rage kwamishinonin ta daga 15 zuwa 9 lamarin da tsohon sakataren raya kogin Kwara mai kasashe tara, Alhaji Bababo Abba, ya ce yayi daidai kuma bai zo da mamaki ba saboda kowace kasa akwai kudin da ya kamata ta biya a shekara amma yawancinsu ba sa biya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG