Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Senegal yayi amanar da cewa zai kara lashe zabe


Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade.
Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade.

Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade, yace yayi imanin cewa zai sake lashe zabe. Wannan wata alama ce dake nuni da cewa yana da niyar sake yin takarar wani wa'adin mulki a watan fabrairu idan Allah ya kaimu, duk da zanga zangar da ake yi a titunan kasar.

Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade yace yayi imanin cewa zai iya sake lashe zabe, frucin dake nuni da cewa yana da niyar yin takarar wani wa'adin mulki a watan Fabrairu idan Allah ya kaimu, duk da zanga zangar kin jinin gwamnatinsa da ake yi.

A wani baban jawabi daya gabatar tun lokacinda aka fara zanga zangar a watan jiya, a ranar alhamis Mr Wade yace a shirye yake ya gudanar da zabe tunda wuri, kafin watan Fabrairun da aka shirya yi, idan masu hamaiya suna son haka.

Yace idan masu hamaiya suna zaton zasu ci zabe, to a shirye yake ya gudanar da zabe cikin kwanaki arba'in ko sittin domin a samu daidaituwa. To amma kuma duk da haka Mr Wade yace, yayi imanin cewa, shine zai lashe zaben.

A watan jiya dubban yan kasar suka yi caa a titunan kasar, wasu suna bore domin nuna rashin amincewa yunkurin da shugaba Wade yake yi na yiwa tsarin mulkin kasar kwaskwarima. Masu hamaiya da dama sun baiyana tsoron cewa canje canjen da aka gabatar da shawarar yiwa tsarin mulkin kasar, zasu sa cikin sauki shugaban ya sake lashe zabe, yasa dansa matsayin da ko ba jima ko ba dade, shine zai gaje shi. To amma shugaba Wade sai ya janye shawarar yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima kafin Majalisar wakilai ta jefa kuri'a.

XS
SM
MD
LG