Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Najeriya Ya Amince da Sayen Abinci da Sutura


Women walk in a street in a residential area in Maiduguri, Borno State May 19, 2013.
Women walk in a street in a residential area in Maiduguri, Borno State May 19, 2013.

Shugaban kasar Najeriya ya amince da a sayi abinci da sutura domin rabawa jihohin dake cikin dokar ta baci

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya bada amincewarsa da a sayi kayan abinci da na almasarufi da sutura domin a rabawa jihohin dake cikin dokar ta baci, wato jihohin Borno, Yobe da Adamawa a arewa maso gabashin kasar inda tashe tashen hankula ya hana su noma.

Gwamnati ta yi la'akari da cewa tashe tashen hankula sun sa yunwa da fatara suna addabar mutanen yankin. Karamin ministan kudi Dr. Yarima Ngama ya ce shugaban kasa ya sauraresu ya bada kudi a sayi wadannan kaya a kaisu jihohi ukun.Misali shugaban ya bada buhun abinci dubu dari uku da casa'in. Kawo yanzu ana bukatar tireloli dari shida da hamsin na daukan abincin da kuma tireloli dari biyar na daukan masara ban da dawa da gyero. Ministan ya kara da cewa sanin kowa ne cewa jihar Borno ita ce tafi yawan jama'a cikin jihohin uku. Ita ce kuma tafi shiga cikin halin kakanikayi da rigingimu.Ta dalilin haka rabin abincin jihar Borno za'a kai. Kashi talatin da hudu za'a kai jihar Yobe. Adamawa zata samu kashi goma sha shida. Har wayau shugaban ya bada nera miliyan dari biyu da hamsin na sayen shinkafa da zannuwa da shadda da kayan masarufi.

Ga karin bayani daga Umar Fark Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG