Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kamfanin Suzuki, Osamu Suzuki Ya Mutu Yana Da Shekaru 94


A karkashin jagorancin dan kasuwar mai kwarjini na tsawon shekaru 40 har zuwa 2021, yawan cinikin kamfanin ya rubanya har sau 10.

Osamu Suzuki, wanda ya bunkasa karamin kamfanin daya shahara wajen kirar motoci zuwa kamfanin kasa da kasa da ya samu dimbin nasarori a kasar Indiya, ya mutu a Larabar da ta gabata yana da shekaru 94 bayan ya sha fama da cutar sankara, kamar yadda kamfanin ya bayyana a yau Juma'a.

A karkashin jagorancin dan kasuwar mai kwarjini na tsawon shekaru 40 har zuwa 2021, yawan cinikin kamfanin ya rubanya har sau 10.

Osuma wanda aka haifa a ranar 30 ga watan Janairun 1930, a yankin Gifu dake tsakiyar kasar Japan, ya yi aure cikin iyalan mutanen da suka assasa kamfanin kafin daga bisani ya zamo shugabansa a 1978.

Ya maida hankalinsa wajen kerar ababen hawan "Kei" marasa nauyi, wadanda galibinsu suka yi shura saboda karancin shan mai da saukin sarrafawarsu

Ya kuma yi kokari wajen neman yin hadin gwiwa da kamfanonin kasa da kasa da damammaki a kasashen ketare domin fadada kasuwancinsa.

Kamfanin kirar motocin ya taba kulla alaka da kamfanonin GM da Volkswagen sannan ya shiga kawancen hannun jari da kamfanin Toyota a shekarar 2019.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG