Faduwar farashin uranium din ta sa shugaban kamfanin na AREVA ya soma kai ziyara a mahakar dake yankin Agadez inda yace ya tarar da ma'aikata ba alamar gajiya duk da matsalolin da suke ciki.
Batun faduwar farashin karfen uranium a kasuwannin duniya, inji Philip, na cikin abubuwan da suka tattauna da shugaban kasar Nijar Mahammadou Issoufou amma suna da kwarin gwuiwar zai sauya nan gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa jami'in dake fafutikar ganin an yi adalci akan ma'adanan kasa, Iliyasu Abubakar ya bayyana cewa a tasa fahimtar faduwar farashin uranium wani abu ne da aka shirya da gangan na cimma wani buri ciki har da batun jinkirta soma mahakar Imurarin.
Yace a wurin na iya fitar da tan dubu biyar duk shekara. Da sunyi alkawarin fara aikin a shekarar 2012. Amma har wa yau babu wanda zai iya cewa ga ranar da za'a soma aikin.Yace tun farko sun yiwa gwamnati hannunka mai sanda. Sun nuna turawan basa son suyi aikin. Yace wata dabara ce ta tanadawa 'ya'yansu domin yau basa bukatan karfen. Dalili ke nan ma da suka karya darajarsa a kasuwannin duniya.
Jamhuriyar Nijar na cikin kasashe uku mafi albarkatun karfen uranium a nahiyar Afirka. Kamfanin AREVA ya shafe shekaru sama da arba'in yana hakowa. Saidai bayanai na nuni da cewa talakawan kasar basa morar arzikin da Allah ya yi masu musamman idan aka yi la'akari da yadda ake jefa kasar cikin wadanda suka fi fama da talauci a duniya.
Yayinda wasu ke ganin ya kamata kasar Nijar ta soke hakar uranium wata kotu a Faransa ta kama dalar Amurka miliyan sittin kudin da ya kamata kamfanin AREVA ya ba kasar Nijar domin jin dadin jama'arta
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.