WASHINGTON DC - A karar daya shigar, Gambaryan ya nemi kotu ta ayyana tsare shi da kwace masa takardun tafiye-tafiyen a matsayin laifin daya saba sashe na 35 karamin sashe (1) dana (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Ya bukaci kotun data umarci ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro da Hukumar EFCC su sake shi tare da dawo masa da takardun tafiye-tafiyensa nan take.
Gambaryan ya kuma bukaci kotun ta wadanda ake karar da wakilansu daga cigaba da tsare shi game da wani bincike ko bukata data shafi kamfanin Binance.
Haka kuma ya bukaci kotun ta umarci wadanda ake karar su nemi gafararsa a bainar jama'a.
Gambaryan ya tabbatar da cewar ya zo Najeriya ne tare da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla wanda ya tsere, domin mutunta gayyatar mashawarcin shugaban najeriya akan harkokin tsaro da Hukumar EFCC da nufin tattaunawa akan ayyukan kamfanin Binance a Najeriya.
Ya cigaba da cewar bai aikata wani laifi ba yayin ganawar, kuma ba'a shaida masa a rubuce wani laifi daya taba aikatawa a Najeriya a matsayinsa na mutum a kowane lokaci.
Gambaryan ya kara da cewar "dalili daya tilo da yasa ake tsare da shine gwamnati na neman bayanai daga Binance kuma tana da bukatu game da kamfanin", inda ya kara da cewar abokin aikinsa nadeem anjarwalla ma ya shigar da makamanciyar wannan kara.
A yayin zaman kotun daya gudana a jiya alhamis, Babban Lauyan Najeriya T.J Krukrubo ne ya tsayawa masu kara a yayin da bangaren wadanda ake karar bai samu wakilcin kowa ba.
krukrubo ya shaidawa kotun cewar an kaiwa bangaren wadanda ake kara sammaci kwanaki 2 da suka gabata.
Jim kadan bayan hakan Krukrubo ya sanarda kotun cewar ya janye daga tsayawa Anjarwalla wanda ya tsere.
Saidai bai bada dalilansa na janyewar ba
Alkalin kotun, Mai Shari'a Inyang Ekwo, ya dage sauraran karar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu mai kamawa.
Dandalin Mu Tattauna