Shugaban Kamaru Paul Biya, ya sha alwashin ganin karshen kungiyar Boko Haram, tare da hana mata shiga kasar Kamaru, wanda a yanzu hakan ke tabbata.
Shugaban na Kamaru, Paul Biya ne ya furta haka a wani jawabi da ya yiwa alumar kasar sa, inda yace Sojojin fiye da dubu bakwai aka girke akan iyakokin Kamaru da Najeriya, a yankin arewa ma nisa.
Paul Biya yace ” maida martini na taron dangi, ga ‘yan ta’adda masamman daga kasashen Afirka, shine amsa ga irin hadarin da kasashen Afirka, ke fuskanta, yana mai cewa wadanda suka tada zaune tsaye a Mali, da wadanda suke kai hare-hare suka hadasa rashin zaman lafiya, a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da wadanda suka kawo tashe-tashen hakula a Mali, suna ci gaba da neman cimma burinsu ta cin mutunci da wulakanci, cikin kasashenmu.”
Ya kara da cewa saboda haka tilas ne mu tashi tsaye mu dauki matakai na murkushesu batare da wani bat a lokaci ba.