Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Kara Farashin Cocoa Don Hana Safararsa Zuwa Wasu Kasashe


Shugabanin kasar Ghana Nana Akufo-Addo yana jawabi a wani taro na manoman Cocoa
Shugabanin kasar Ghana Nana Akufo-Addo yana jawabi a wani taro na manoman Cocoa

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar da karin fiye da sittin cikin dari a farashin da take sayen cocoa daga hannun manoman kasar, a kokarinta na neman shawo kan matsalar safarar cocoa zuwa wasu kasashen da ke makwabtaka.

KUMASI, GHANA - Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya fitar da wannan sanarwar a yayin wani taron kaddamar da shirin cocoa na shekarar 2023 zuwa 2024 a garin Tepa' daya daga cikin garuruwan da ake noman cocoa a kasar Ghana.

Akufo-Addo ya ce "a yau farashin ma'aunin cocoa tan daya ya tashi daga sidi 12,800 zuwa 20,943 kwatankwacin $1,837 na dalar Amurka. Karin da ba'a taba yi wa manoman cocoa a Afrika ta Yamma ba a cikin shekaru hamsin da suka shude."

Shugabanin kasar Ghana Nana Akufo-Addo a wani taro da manoman Cocoa
Shugabanin kasar Ghana Nana Akufo-Addo a wani taro da manoman Cocoa

Masu ruwa da tsaki bisa harkar cocoa a Ghana sun yi marhabin da wannan matakin na kara kashi 63.5 ciki dari a farashin cocoa da gwamnati ke siya a hannun manoma.

Saeed Sulaiman wani mai nazarin harkar a kasar ya ce " wannan kari gaskiya zai taimaka sosai wajen hana manoma mika gonakinsu ga masu hakar zinari saboda matsalar rashin isashen kudaden shiga."

Ya ci gaba da cewa "safarar cocoa zuwa kasashen waje da suke yi duk saboda rashin isashen kudaden shiga ne ya kaisu ga aiwatar da hakan. Saboda in ka kwatanta farashin da ake sayen cocoa a hannun manoma a Ghana da farashin a wadannan kasashen za ka ga cewa na su ya fi na Ghana. Abinda ya janyo fasa kaurin cocoa zuwa kasashen waje kenan."

Mata masu aikin gyara Cocoa a Ghana
Mata masu aikin gyara Cocoa a Ghana

Wani rahoton da hukumar kula da cocoa ta kasar Ghana COCOBOD ta fitar ya nuna cewa kasar ta yi asarar kusan miliyan 600 na dalar Amurka a bara sakamakon safarar cocoa zuwa wasu kasashe kamar Togo da Burkina Faso ba bisa ka ida ba.

Rahoton ya kuma kara da cewa tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 Ghana ta yi asarar filayen noman cocoa hectar dubu goma sha tara zuwa ashirin sakamakon hakar ma'adinai a kansu.

Buhuhunan Cocoa a Ghana
Buhuhunan Cocoa a Ghana

Hukumar COCOBOD ta kasar ta bayyana cewa tana sa ran samun cocoa ma'aunin metric tan 820,000 daga manoma tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024 inji Fiifi Boafo, mai magana da yawun hukumar a Ghana.

Ghana ita ce kasa ta biyu da aka fi samar da cocoa a duniya bayan Cote Divoire, amma matsalar safarar cocoa tare da hakar ma'adinai a filayen cocoa na haifar da koma baya wajen samar da isashen cocoa da ke baiwa kasar kudaden shiga.

-Hamza Adam

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG