A lokacin daya kai ziyara Lagos, Shugaba Macron ya ziyarci gidan rawa na fitaccen mawakin nan Maikare hakkin Talakawa Marigayi Fele Anikula Kuti, inda yayi jawabi ga daruruwan yan Najeriya da ke gidan rawan, ciki kuwa harda gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode. Macron yace akwai bukatar shugabannnin Afrika su tashi tsaye wajen raya kasashen su, domin kuwa nahiyar ba zata ci gaba ba sai da hanun yan Afrika.
Da aka tambayi shugaban na Faransa ko menene zaice game da ziyarar sa gidan Fela? sai yace, "wannan wuri yana da mahinmanci gare ni, inason zuwan sa ,kuma abin alfahari ne ga kowa na gana da gwamman jiha da Yayan Fela irinsu Femi"
Shi kuwa Femi daya daga cikin 'ya'yan marigayi Fela da shima yake tashe a irin salon wakar mahaifinsa, yace. "abin alfahari ne ga mahaifin mu daya shafe shekara da shekaru yana yakin neman yancin biladama da wannan gida".
Wadansu 'yan Najeriya da Niger da Sashen Hausa ya yi hira da su dangane da wannan ziyarar sun bayyana gamsuwa da ziyarar da suka ce zata kara dankon zumunci tsakanin kasa da kasa da kuma kara fahimtar juna.
Kafin shugaban na Faransa ya bar Najeriya saida ya rattaba hannu a wani shirin tallafin kudin raya kasa ga Najeriya na Dala miliyan 475 domin aiyukan raya kasa a jihohin kano da lagos da ogun.
Saurari rahoton da Babangida Jibril ya aiko daga Lagos
Facebook Forum