Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Harajin Wayoyin Sadarwa Na Kashi 5%  Da Harajin Kayan Da Ake Sarrafawa A Cikin Gida


Tinubu ya ya dauki wani muhimmin mataki na baiwa ‘yan Najeriya fifiko ta hanyar sanya hannu kan wasu dokoki guda hudu.
Tinubu ya ya dauki wani muhimmin mataki na baiwa ‘yan Najeriya fifiko ta hanyar sanya hannu kan wasu dokoki guda hudu.

Cikin wani muhimmin matakin da Shugaban na Najeriya ya dauka, Bola Ahmed Tinubu ya dauki wani muhimmin mataki na baiwa ‘yan Najeriya fifiko da kuma magance manufofin kasafin kudi da ba su dace da kasuwanci ba ta hanyar sanya hannu kan wasu dokoki guda hudu.

Dele Alake, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru wanda ya bayyana haka ga manema labarai ya fada ranar Alhamis cewa ,shugaban ya sanya hannu kan dokokin

Daga ciki akwai dakatar da harajin kashi 5% na ayyukan sadarwa da kuma harajin fitar da kayayyaki na cikin gida.

Shugaba Tinubu har ilayau ya sa hannu a kan dokar kudi ta 2023, wadda a yanzu ta jingine fara aiki da sauye-sauyen da ke cikin dokar daga ranar 23 ga Mayun 2023 zuwa 1 ga Satumban 2023.

Shugaba Tinubu ya kuma rattaba hannu a kan dokar karbar harajin shigo da kaya da aka yi wa garambawul ta 2023, wanda a yanzu zata fara aiki daga 27 ga watan Maris zuwa 1 ga Agustan 2023.

Tinubu ya kuma bayar da umarnin dakatar da wani sabon haraji mai suna Green Tax da aka bullo da shi kan robobin da ake amfani da su da wani nau'in haraji da ake karba a kan wasu motoci da ake shigowa da su kasar.

Bugu da kari, shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar Kudi, wanda zai jinkirta ranar fara canje-canjen da aka tsara a cikin dokar daga Mayu 23, 2023, zuwa Satumba 1, 2023, hakan zai yi daidai da mafi karancin kwanaki 90.

Shugaba Tinubu ya kuma rattaba hannu kan dokar garambawul na kudin harajin kwastam, 2023, inda ya sauya ranar fara canjin haraji daga ranar 27 ga Maris, 2023, zuwa 1 ga Agusta, 2023.

Alake ya nanata matsayar shugaban kasar, inda ya bayyana cewa gwamnati ta amince da masu kasuwanci, na gida da na waje, a matsayin muhimman abubuwan da ke haifar da karuwar GDP da samar da ayyukan yi. Gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da tsare-tsare masu kyau da kuma samar da abubuwan kara kuzari don samar da yanayi mai kyau na kasuwanci don bunkasa a cikin kasar.

Alake ya bayyana ce wa, Shugaba Bola Tinubu na fatan tabbatar wa ‘yan Najeriya da suka damka masa amanar mulki cewa, ba za a sake samun wani nauyi na haraji ko ka’idojin kasuwanci da ke hana ci gaban tattalin arziki ba.

Gwamnati ta ci gaba da sadaukar da kai don magance korafe-korafe da samar da yanayin da zai inganta ci gaban kasuwanci, samar da ayyukan yi, da ci gaban tattalin arziki gaba daya.

~ Yusufuddeen Aminu

XS
SM
MD
LG