A wani al’amari mai ban mamaki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya dauki matakin dakatar da Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa na shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya tura wa manema labarai, ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayar da izinin dakatarwar ne domin a samun cikakken bincike kan yadda Bawa ya gudanar da ayyukan hukumar a lokacinsa.
A bisa umarnin shugaba Tinubu, an umurci Bawa ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar. Wannan tsari zai ba da damar ci gaba da aiki a ofishin shugaban hukumar har sai an kammala bincike.
Ko a jawabin da ya yi bayan da aka rantsar da shi a watan Mayu, Tinubu ya ambato bukatar magance matsalar cin hanci da rashawa da almundahana a Najeriya.
Hukumar EFCC dai na taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun kudaden kasa da kuma tabbatar da cewa an magance matsalolin da ke yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, hankulan 'yan Najeriya da dama sun karkata kan yadda wannan al'amari zai kaya.
Wasu dama da na ganin, sakamakon wannan bincike zai yi tasiri ga makomar hukumar ta EFCC da kuma yadda za a fadada batun yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Yusuf Aminu Yusuf.