Da sanyin safiyar Asabar shugaba Barack Obama na Amirka yayi kira ga shugabanin Burundi da su yiwa Allah su halarci shawarwarin da za'a yi da nufin kawo karshen rikicin siyasar kasar da kuma kawo karshen kamarin tarzoma.
Shugaban yayi wannn furucin ne ta sakon da aka dauka akan faifain vidiyo da aka gabatar ko kuma aka nunawa yan kasar Burundi a ranar Asabar.
Shugaba Obama yace kashe wadanda basu san hauwa ba, basu san sauka ba, da kuma yayata kalamomin tsana ko kum wadanda zasu harzuka mutane da shugabanin kasar ke yi suna dagula makomar kasar.
A saboda haka yayi kira ga gwamnatin kasar ta kawo karshen yin haka ta halarci taron da kasa da kasa ke shiga tsakani. Haka kuma Mr Obama yayi kira ga yan kasar da suyi watsi da tarzoma su yin aikin hada kan 'yan kasar.
Yace bayan yakin basasa suna aikin sake gina kasar su. Sun ga alfanun yiwuwar samun makoma mai alheri. A saboda haka yace kada su yarda sabanin siyasa da masu yayata tsana su sa kasar komawa baya.
A ranar Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da wani kuduri daya bukaci gwamnatin Burundi tayi shawarwari da masu hamaiya . Shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda ne zai shiga tsakani a madadin kasashen Afrika ta gabas.