Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya ta FIFA Giani Infantino, ya yi tir da haramcin da gwamnatin Iran ta dorawa mata masu zuwa kallon wasa zuwa filayen wasan kasar kuma yace bai dace ba a dauki irin wannan mataki ba.
Gwamnatin Iran ta haramtawa mata zuwa filayen wasa ne bayan juyin juya halin kasar a shekarar 1979. Kungiyar kare hakkin bil adama ta “Human Rights Watch” da kuma hukumar FIFA sun kira da a dage wannan haramci.
CNN ya tuntubi hukumar kwallon kafar kasar Iran ta FFIRI da gwamnatin Iran domin jin ta bakinsu a kan wannan batu. Kiran da Infantino ya yi na zuwa ne jim kadan bayan mutuwar Sahar Khodyayari, wata mace mai sha’awar wasa kwallo da ta cinnawa kanta wuta bayan an hanata shiga filin wasa a birnin Tehran.
Hukumar FIFA tayi kira da a baiwa matan Iran masu sha’awar wasan kwallon kafa dama su je kallo.
A wata sanarwa da ya sanyawa hannu, Infantino yace yana sa ran hukumar kwallon kafar Iran da sauran hukumomin kasar zasu duba wannan batu su magance shi.
Sai dai yace akwai wakilai da FIFA ta tura a Iran a halin yanzu kuma suna saurare su ji labari mai dadi.
Facebook Forum