Shugaban Amurka Donald Trump, a jiya Litini, ya sake wallafa wani hoton kansa da wani kwararren mai zane dan Najeriya, wanda aka fi sani a kafar twitter da sunan Creative Doks, ya zana.
Mai zanen ya ce wannan hoton nasa shi ne na biyu da ya zana na Shugaban na Amurka, ya kuma kara da cewa ya kwashe sa'o'i 70 yana amfani da wani alkalami na mussaman don zana hoton mai tsawon inci 24 da kuma fadin 21 inci.
"Wannan ne hoto na biyu na Shugaba Trump da na zana. A wannan karon ina matukar son ya gani… Don Allah a yi ta sanyawa a kafar twitter har sai Shugaban ya gani," sakon da ke tafe da hoton kenan a shafin twita.
Amma shugaban, wanda aka fi sani da son wallafa labarai a shafinsa na twita, ya nuna alamar ya gani kuma ya amsa. "Ya Doks Art, ba wai kawai na ga hoton ba ne, ya na da ban sha’awa matukka. Kai shahararren mai zane zane ne, kar ka fasa burinka!”
An sake tura wannan sakon na Trump har sau fiye da 27, 500 a kafar twita.
Wannan shi ne karo na biyu da Trump yake alaka da wani dan Afirka ta hanyar twita. Watannin baya, ya sake bidiyo na wata mata yar wasan kwallon kafa.
Facebook Forum