Shugaban Najeriya Muhmmadu Buhari ya rubuta wa shugabannin kasashen duniya da kungiyoyi wasikar godiya saboda taimakon da suka ba kasar wajan kawar da cutar Shan Inna da ake kira Polio da turanci, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin ganin cutar ba ta dawo ba kuma bayan haka za a inganta tsarin kiwon lafiyar kasar, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu ya tura wa manema labarai.
Shugaban ya kuma jinjina wa mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban kwamitin kawar da cutar Shan inna a Najeriya, tare da ‘yan kwamitin saboda wannan nasarar da Najeriya ta samu da kuma ceto yaran kasar daga cutar Shan inna.
Shugaba Buhari ya kuma rubuta wasikun godiya dabam daban zuwa ga Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad III, da Bill Gates, da kungiyar Tarayyar Turai, da Shugabar Jamus Angela Merkel, da babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Tedros Ghebreyesus, da sauransu.
Wannan wasikar na zuwa ne bayan da aka ayyana Najeriya a matsayin kasar da ta rabu da cutar Shan inna.
Facebook Forum