Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa Kaycee Madu wani dan Najeriya murnar nada shi matsayin Ministan shari’a kuma babban jami’in shari’ar gwamnatin lardin Alberta a kasar Canada, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba Shugaban Najeriya shawara na musamman, Femi Adesina.
Madu ya yi abun tarihi a matsayin dan Afrika da aka nada Ministan lardi a tarihin Canada, kuma shine Sakataren lardi da ke rike da hatimin lardin Alberta.
Shugaba Buhari ya bayyana wannan karramawar a matsayin “gagaruma a tarihi,” ya na mai cewa hakan ya sake karrama ‘yan Najeriya a matsayin masu hazaka, da ke bayyana kansu ta fannonin rayuwa dabam daban.
Shugaban ya ce a matayinsa bakar fata na farko da aka ba mukamin Ministan shari’a kuma Attoni janar a Canada, Madu ya shiga littattafan tarihi, Shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya, a gida da waje, da su ci gaba da kasancewa wakilan kasarsu na gari.
Facebook Forum