Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya isa birnin Sakkwato hedikwatar jahar Sakkwato don yin ta'aziyyarsa ga iyalan tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar Juma'a.
Gwamnan jahar sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da sauran mukarabbanshi suka tare Shugaba Buharin, tun bayan saukar shi a filin jirgin saman Sultan Abubakar na lll da ke sakkato, ya wuce gidan marigayin da ke unguwar Sama Road, bayan tattaunawa da ya yi da iyalan mamacin.
Gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya gabatar da jawabin shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce Shugaba Buhari na jajantawa iyalai da jama'ar jahar, kuma ya kara da cewa "zan kafa wata cibiya don tunawa da abubuwan da mamacin ya yi ma kasa" domin kuwa tarihin kasar bazai cika ba ba tare da an anbato marigayin ba.
Bayan ta'aziyyar Shugaba Buhari ya hau jirgi ya koma birnin tarayya. Alhaji Bashir Gidado, kwamishina a jahar ta Sakkwato, ya yi magana a madadin gwamnatin jahar ta Sakkwato, da cewa wannan ziyarar ta shugaban kasa ta zo a dai-dai lokacin da ya kamata duk kuwa da yadda ake ta sukar rashin zuwan nasa a jiya lokacin jana'iza, kuma suna ma shi godiya da fatan Allah ya kai shi gida lafiya.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyyina daga Sakkawaton.
Facebook Forum