Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Isa Dubai Don Halartar Taron Baje Kolin Fasahar Kasashen Duniya


Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 dake gudana a hadaddiyar daular laraba
Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 dake gudana a hadaddiyar daular laraba

Ana sa ran taron zai ba Najeriya damar kulla kawance mai ma’ana da kasashe sama da 190 a fadin duniya da suka halarci taron na kwanaki uku a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adesina ya fitar a jiya Laraba, ya bayyana cewa taron bikin baje kolin na 2020 zai bayar da dama ga wakilan Najeriya domin nuna gagarumin ci gaban da aka samu ta fannin tattalin arziki a cikin shekaru shida da suka gabata.

Sanarwar ta ce hakan zai kuma kasance wani gimshiki na mayar da kasar muhimmiyar makoma ta zuba jari kai tsaye daga kasashen ketare.

Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 a hadaddiyar daular laraba
Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 a hadaddiyar daular laraba

Baya ga rangadin da za’a yi a rumfar Najeriya a bikin baje kolin, shugaba Buhari zai karbi bakuncin masu son zuba jari a kasarsa tare da ganawa da mai martaba Sarkin Dubai Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, da kuma Yarima mai jiran gadon masarautar Abu Dhabi Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

Shugaba Buhari dai ya sami rakiyar wasu daga cikin manyan mukarrabansa, ciki har da ministoci 10.

A ranar Asabar shugaban zai kasance babban bako na musamman a dandalin kasuwanci da zuba jari da zai soma daga gobe Juma'a.

Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 a hadaddiyar daular laraba
Shugaba Buhari a Taron EXPO 2020 a hadaddiyar daular laraba

Ana sa ran dawowar shugaba Buhari gida Abuja a ranar Lahadi 5 ga watan Disamba wanda ya yi daidai da ranar da Kamfanin jiragen sama na hadaddiyar Daular Larabawar wato Emirates, ya ba da sanarwar dawowa da zirga-zirgar fasinjoji tsakanin Dubai da Najeriya, bayan shafe tsawon watanni da dakatar da aiki tsakanin kasashen biyu matakin da ake ganin ya biyo bayan sasancin da aka samu.

XS
SM
MD
LG