Yau shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya gana da gwamnonin jihohin Najeriya.
Gwamnonin sun kawo masa ziyarar fatan alheri ne tare da yi masa murnar samun koshin lafiya.
Sun yi anfani da ziyarar sun yi masa godiya ta musamman akan dokin da ya basu wanda ya fitar dasu daga kasa biyan albashi da alawus da kuma samar da hanyoyin bunkasa noma domin inganta rayuwar al'umma.
Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, shugaban kungiyar gwamnonin yace babban makasudin ziyararsu shi ne su yiwa shugaban barka da zuwa tare da yi masa godiya. Sun kara tabbatar wa shugaban suna tare kuma zasu taimaka ta kowace hanya.
Akan cewa duk da taimakon da shugaban kasa ya ba jihohin wasunsu har yanzu basu biya albashi ba. Gwamna Yari ya ta'allaka hakan da raguwar kason da suke samu daga gwamnatin tarayya da faduwar Nera.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum