Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa shugabannin majalisun dokokin tarayya rashin jin dadin dangantaka tsakanin shi da yan majalisar a wa’adin mulkinsa na farko.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin walimar dare kafin tashinsa zuwa Umura a Saudiya. Bisa ga cewarsa, rashin kyakkytawar dangantaka tsakaninshi da majalisa ya kawo cikas a harkokin mulki da ci gaban Najeriya baki daya.
Sai dai a hirarsu da Sashen Hausa, masu sharhi a harkokin yau da kullun sun bayyana cewa, rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin shugaban kasa da majalisar bashi da alaka da matsalolin da ake fuskanta a kasar a halin yanzu. A bayaninsa, Auwal Musa Rafsanjani, yace.
“Wannan bayani da shugaban kasa yayi kamar an yi san rai, idan aka yi la’akari da cewa majalisar dokokin Najeriya ta taka rawar gani wajen inganta harkokin ci gaban kasa kamar su, tattalin arzki, da gyara harkar zabe. Saboda haka bai kmaata ace an basu alhakin matsalolin da Najeriya ke fuskanta ba"
A nashi bayanin, Malam Sha’aibu Mungadi, dan jarida mai sharhi a Najeriya yace ai damokaradiya ne, bangaren doka ya yi tsayin daka wajen ganin an yi abinda zai kawo ci gaban al'umma ba abinda gwamnati mai ci ke so ba.
“Sanin kowa ne dama akan sami sabani tsakanin bangaren gwamnati da Majalisar Dokoki, wanda har wasu suna cewa idan aka sami jituwa sosai tsakain gwamnati da 'yan Majalisa to za’a iya samun matsala sosai a kasa, domin kuwa hakkin majalisar ne ta takawa gwamnati birki domin samun ci gaban kasa"
Saurari cikakken rahoton Umar Faruk.
Facebook Forum