Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Amince da Biyan Kudin Makarantar 'Yan Matan Chibok


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A watan Afirilun shekarar 2014 ne 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan makarantar sakandaren mata dake Chibok 276 yayinda wasunsu suka tsere, wasu kuma aka cetosu da saura a hannun 'yan ta'addan, gwamnatin Najeriya tana kula da karatun wadanda suka kubuta.

Amincewa da fitar da kudi Naira miliyan 164 da shugaba Muhammad Buhari ya yi domin biyan kudin 'yan matan Chibok dake karatu a jami'ar ABTI dake Yola ya nuna yadda gwamnatin tarayya ke kulawa da matan da suka samu 'yanci tare da kwantar masu da hankali a makarantar da 'ya'yan masu hannu da shuni ne suke samun zuwa.

Kalilan daga cikin 'yan matan da suka samu 'yanci sun samu tafiya kasar Amurka karatu amma yanzu yawancinsu suna jami'ar ABTI wadda mallakar tsohon mataimakin shugaban Najeriya ne, Alhaji Atiku Abubakar.

Gwamnatin Najeriya ta hannun ministar mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta bayyana dalilan da suka sa ta tura duka 'yan matan jami'ar ABTI, mai zaman kanta. A cewarta ABTI ita ce kadai jami'a daya tilo da take da tsarin karatun da ya dace da 'yan matan domin su samu natsuwa su yi karatunsu. Ta kara da cewa mata 57 da suka tura wasu makarantu a Jos da Zaria sai da suka maida dukansu ABTI saboda makarantun sun ce basu da irin tsarin ABTI da zai taimakawa matan.

Yusuf Ishaq Baji wani dan jarida ya ce biyan Nera miliyan 164 da gwamnatin tarayya ta yi a madadin 'yan matan wa jami'ar ABTI tamkar ita gwamnatin bata da kwarin gwuiwa ne akan nata jam'o'in ne.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG