Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Na da Sauran Damar Gyara Najeriya –Bafarawa


Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa
Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa

Biyo bayan caccakar da tsohon shugaba Jonathan ya yiwa Shugaba Buhari cewa ya gaza, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya ce shugaban na da sauran damar gyara Najeriya tun da yanzu ya samu lafiya

Bayan kalubalantar gwamnatin Buhari da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya yi da cewa ta gaza, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce shugaba Muhammadu Buhari na da sauran damar gyara Najeriya.

Bafarawa ya yi furucin ne yayinda yake zantawa da manema labarai a Abuja inda ya ce bai gamsu da ikirarin gwamnatin Buhari ba na cewa ta samar da ingantacen tsaro. Ya yi misali da yawan satar mutane da labaran yadda Boko Haram kan kai hare-hare.

Bafarawa ya ce a matsayinsa na dan kasa ya na da damar ya ba shugabansa Buhari shawara amma kuma bin shawarar ya rage ga shugaban.

Duk da cewa gwamnati na ikirarin samun tsaro, Bafarawa ya ce maganar fatar baki ce kawai domin talakawan kasar basu gani a kasa ba. Ya ce yanzu mutane na tsoron shiga mota daga Kaduna zuwa Abuja, jirgi suke shiga saboda tsoron masu sace mutane.

Amma babban sakataren APC, jam’iyyar dake mulki, Alhaji Mai Mala Boni ya ce gwamnati ta yi duk abun da ya dace har da tsaro dake cikin samun nasara. Ya ce ba sa mamaki idan dan PDP ne ya fito yana sukar gwamnatin yanzu. Yace a lokacin gwamnatin PDP, Masallaci ko Coci ba’a isa a shiga ba saboda tabarbarewar tsaro. A lokacin gwamnatin PDP hatta kudaden sayen makamai sace su aka yi. Sakataren yace barnar da ‘yan PDP suka yi ne Shugaba Buhari yake gyarawa a yanzu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG