Babbar jam’iyyar adawa a Sakkwato, APC, ta zargi jam’iyya mai mulki da huce haushin cin zabe da kyar kan wasu ma’aikatan gwamnatin jahar. APC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa wannan lamari na uzzura wa ma’aikatan gwamnati da ake zargin sun goyi bayan jam’iyyar ta APC a zaben da ya gabata, ya fi Kamari a wasu manyan ma’aikatun gwamnati, da kuma kananan hukumomi. Abin bai tsaya ga ma’aikatan gwamnati ba, ya zarce har ya zuwa ‘yan kasuwa da ma daidaikun jama’a ta hanyoyi daban-daban.
Shugaban jam’iyyar APC din na jahar Sakkwato, Isah Sadiq Achida, ya kuma yi jawabi ga wani taron manema labarai domin kokawa akan lamarin. Ya ce wannan bi ta da kullin siyasa ya hada da rike albashi da sauya wuraren aiki ko kuma cire su daga irin aikin da su ke yi ba tare da ba su wani aikin na dabam ba, duk da zummar dai a kuntata masu, saboda zargin sun goyi bayan APC a zaben da ya gabata.
Alhaji Achida ya ce, “ Abubuwan sun kai har inda aka hana talakawa diban ruwa a rijiyoyin da aka gina da kudaden al’umma; an hana wasu ‘yan kasuwa su baje haja a kasuwanni, an kuma kwace ma wasu shuguna ba don sun aikata wani laifi ba, ba don rashin biyan haraji ba.”
To sai dai bangaren gwamnatin jahar ya musanta akasarin zarge-zargen, duk da yake, a ta bakin wani tsohon dan majalisar dokoki kuma mashawarci na musamman ga gwamna, Bello Malami Tambuwal, aikin gwamnati ya na iya kai mutum a ko ina. Ya ce duk lokacin da aka samu sabuwar gwamnati sabbin shugabannin kan nada wasu amintattu da za su taimaka masu. Ya ce dama shi aikin gwamnati ya gaji haka. Hasali ma, in ji Malami, akwai wasu bayanannun ‘yan APC din da har yanzu su na daiki tare da gwamna.
Ga Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:
Facebook Forum