Shirin dai zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin Najeriya da samar da wadataccen abinci ga al’ummar kasar baki daya, har ma da wasu kasashen Afirka da ke makwabtaka da ita. Banda haka kuma, shirin zai inganta danganta da ke tsakanin kasashen biyu
Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara a Najeriya ya bayyana cewa kasar Ukraine na da ilimin kimiyya da fasahohin zamani da za su taimaka wajen tababbatar da manufar ta a Najeriya.
A hirarshi da Muryar Amurka, Dakta Mohammad Mahmud Abubakar, ya ce kasar za ta zama wata cibiya da sauran kasashe Afirka za su amfana wajen samun duk wani iri na hatsi, kazalika ya yi kari da cewa, a shirye Najeriya take ta ba Ukraine hadin kai dari bisa dari wajen samar da tasoshin da za’a rika tara hatsin.
A nasu bangaren, wasu manoma a Najeriya suna kyautata zaton shirin zai bunkasa sana'arsu.
Ana sa ran isowar hatsin da Ukraine ta yi alkawarin bawa Najeriya a wata mai kamawa karkashin shirinta mai taken "Grains from Ukraine," duk kuwa da yakin da ake ci gaba da gwabzawa tasakanin kasar da Rasha wanda ya shafi karfin tattalin arzikinta.
A nasa bayanin, masanin tattalin arziki Dakta Isa Abdullahi ya ce wannan yunkuri na kasar Unraine zai taimaka wa Najeriya wajen samar da wadataccen abinci da rage tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta a halin yanzu.
A nahiyar Afirka, Najeriya na daga cikin kasashen da Ukraine ta dauka a matsayin babbar abokiyar kasuwancinta, abinda ya sa kasar daukar wannan mataki na inganta dangantakar da ke tsakani. kasashen.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim: