Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ya Dace a Saurari Shari’a Ta Yanar Gizo a Najeriya?


Babbar kotun tarayyar Najeriya ta ayyana sabbin ka’idojin sauraron shari’a ta yanar gizo sakamakon yadda annobar coronavirus ta tilastawa kasashen duniya gudanar da sauyi a dukannin bangarorin rayuwa.

Wadannan sabbin ka’idojin aiki da suka kunshi neman amincewar bangarorin da ake tuhuma da lauyoyinsu da kuma ba wa mai shari’a damar sauraron kararraki 9 a rana sun fara aiki ne a ranar 18 ga watan Mayun nan.

Tun bayan ambata shirin fara sauraron shari’a ta yanar gizo da babban kotun tarayya ta bakin mai shari’a John tsoho ta ayyana tare da fitar da sabbin ka’idojin aiki ne ‘yan Najeriya suka fara fashin baki a kan yiyuwar aiwatar da wannan tsari na zaman kotu ta yanar gizo la’akkari da yadda ake samun jinkiri a zaman kotu na gar-da-gar.

Shugaban tsangayar koyar da aikin lauya na jami’ar Nile da ke birnin Abuja, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru, ya ce akwai matsala tattare da sauraron shari’a ta yanar gizo saboda rashin tanadi a karkashin doka tun farko.

A wani bangare kuma, wani fitaccen dan jarida kuma dan kasuwa, Mungadi Shu’aibu, ya danganta batun yin shari’a a yanar gizo da cewa.

Ita kuwa wata fitaciyyar lauya, Barrister Halima Yusuf ta bayyana cewa, gudanar da ayyukan shari’a ta yanar gizo zai taimaka wajen kamalla aiki a kan lokaci.

Kazalika, wani fitaccen dan kasuwa kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar NPM, Mustapha Bala Getso, cewa ya yi batun gudanar da shari’a ta yanar gizo ba zai ciyar da kasar nan gaba ba.

Ana dai ci gaba da tafka muhawara a kan wannan batu a matakai daban-daban inda wasu ‘yan kasar ke marawa matakin baya yayin da wasu ke yin watsi da matakin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG