A jiya Litinin ne ma ,kasashen Saudiya da Masar da Baharain da kuma Daular Larabawa suka sanar da katse huldar diplomasiyyarsu da kasar Qatar a bisa zarginta da tallafawa ayyukan ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da Al-Qaida da ISIS da Kungiyar 'Yan uwa Musulmi kana kuma da ma yin katsalandan a cikn harkokin cikin gidansu.
Baya ga wannan ma an kori kasar ta Qatar daga rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiya ke jagoranta a yakin kasar Yemen.
Wannan dambarwa a fagen diplomasiyyar kasashen na Larabawa na zuwa ne a kasa da kwanaki 15 bayan ziyarar da Shugaban Amurka Trump ya kai Saudiya inda ya bukaci kasashen Musulmi da su dauki kwararan matakai wajen yaki da kaifin kishin Islama.
To sai dai kuma masana tattalin arziki da diflomasiya irinsu Abdullahi Prembe na ganin akwai lauje cikin nadi.
Masanin dai na ganin wannan janyewar ka iya shafan ita kanta kasar Qatar ganin cewa ko a baya akwai wasu kasashe da suka fuskanci takunkumi.
Ya zuwa yanzu tuni Qatar din ta musanta zargin marawa 'yan ta'addan baya da suka hada da kungiyar ISIS, inda ta ce matakin ' ba shi da tushe' .kuma tuni aka dakatar da jiragen saman kasar Qatar bi ta sararin samaniyar kasashen Masar da Saudiya, yayinda aka cigaba da takun sakar dake barazana ga manayn harkokin sufurin sama.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum