Kungiyar Tottenham ta yi wata ganawa akan ko dan wasa Gareth Bale zai koma kungiyar, amma kulob din na shakku kan damar da suke da ita game da sayen dan wasan na Real Madrid.
Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Spurs ta binciki yiwuwar neman tsohon dan wasan nasu ya dawo arewacin Landan, amma lura da kudaden da aka sanya hannu kan yarjejeniyar, akwai alama lamarin ba zai yi wu Bale ya koma gasar Firimiya ba kafin a kammala gasar a ranar Juma'a.
Yunkurin kungiyar na siyan dan wasan AC Milan ne Krzysztof Piatek bai cimma nasara ba, cikin sa'o'i 24 na karshe kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa, kamar yadda kungiyar Spurs ta yi watsi da dan wasan Poland din ga tsohon gwarzo Jurgen Klinsmann, wanda shi ne manajan Hertha Berlin.
Makudan kudaden albashi da ake biyan shi a duk mako na £ 600,000 shi ne babbar matsala tsakanin Spurs ta kammala cinikin dan wasan Wales.
Tottenham ta san cewa ba za su iya kusantar albashin da dan wasan yake dauka ba, kuma tattaunawar ta tanadi yadda za a tsara yarjejeniya da Real don gamsar da dukkanin bangarorin.
Amma yawan kudaden shiga na nuna cewa yana da wuya kusan Tottenham za ta iya cire abin da ba shakka zai kasance mafi kyawun ciniki a kasuwar siye da siyarwa ta Janairu.
Facebook Forum